Taken taron shi ne ‘Zaman Lafiya daga Gida Yake Farawa”. Kodayake shugabar kungiyar ta Global Women,Hajiya Amina Namadi Sambo, bata kasance a taron ba amma ta samu wakilcin Nafisatu Nuhu Babajo.
Kungiyar ta ce zata fito da dabaru da hanyoyin wanzar da zaman lafiya kuma zata yi amfani ne da mata. Wakiliyar Amina Namadi Sambo, Nafisatu Babajo ta ce suna da wani shiri dake cewa “Peace begins at home”, ma’ana zaman lafiya daga gida yake farawa. Idan aka samu zaman lafiya da kyakyawar tarbiya da fahimta tun daga gida to zai shafi dukkan al’umma, inji Nafisatu. Ta kara da cewa daga gida ake samun matsala.
A cikin manyan mata da suka kasance a taron akwai kwararru irinsu Dr Dayyaba Sha’aibu da Hajiya Rabi Abdullahi Bincham.
Dr Sha’aibu tayi karin haske akan taken taron ta ce kodayake maza su ne kai amma a zahiri mata su ne wuya kuma duk inda suka ga dama zasu karkata kan. Ta ce idan mace bata damu mijinta ba da bukatu ko matsaloli hankalinsa zai kwanta, za’a yi zaman lafiya. Yara zasu tashi su ga iyayensu da zaman lafiya su ma haka zasu yi idan sun yi aure. Injita duk tashin hankali, tashin bamabamai, shaye-shaye da dai sauransu duk zasu ragu.
Shugabar tsara ayyukan kungiyar Hajiya Rabi Abdullahi Binchan tayi tsokaci akan matakin da kungiyar zata dauka nan gaba. Tace sun ji labarin Garin Damagaza, karamar Abuja dake kusa da Abuja inda akwai kabilu daban daban da addinai daban daban amma suna zaman lafiya da juna. Saboda haka, inji Hajiya Rabi zasu nemi matasan garin su ilimantar dasu domin aikinsu ya zo masu da sauki.
Ita ma shugabar matar Damagaza ta kasance a taron da mata fiye da dari biyu. Tace su basu da matsala domin an fadakar dasu akan zaman lafiya.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum