Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Maharba Na Neman Izinin Gwabzawa Da Boko Haram


Wasu maharba
Wasu maharba

Duk da shakkun da wasu 'yan Najeriya ke nuna game da barin maharba su fafata da 'yan Boko Haram, maharban sun sake gabatar da bukatarsu ta a barsu su buga da 'yan bindigar.

Kungiyar Maharba a jahar Borno ta bukaci a ba ta izinin gwabzawa da mayakan Boko Haram. ‘Yan kungiyar sun ce a shirye su ke su buga da mayakan Boko Haram muddun aka ba su kayan fada da kuma izinin fantsama cikin dajin Sambisa, inda ‘yan Boko Haram fagewa.

Kungiyar Maharban, ta bakin Sarkin Bakan Jahar Borno, ta ce ta jima ta na neman goyon bayan gwamnati don tinkarar ‘yan Boko Haram, ta na mai jaddada cewa babu wani lungu a dajin da ba ta sani ba.

Cikin maharan da ke tsumar shiga dajin Sambisar har da wata mace, mai suna Hajiya Maira Maidunoma, wadda ta ce ta gaji farautar ce daga mahaifinta, ta ce ita ma ta yi damarar abkawa cikin dajin na Sambisa don bugawa da ‘yan Boko Haram.

Ga wakilinmu a shiyyar Borno, Haruna Dauda, da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG