Bincike ya nuna da cewar 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, da yawa na fama da jinya a shirin da kulob din ke yi na fafatawa gasar firimiya lig mako na 19, inda za ta ziyarci Brighton a ranar Laraba 26 ga watan Disamba.
Masu fama da jinyar wanda hakan yasa ba za su buga wasa a karawar ranar Laraba ba, sun hada da Rob Holding da Konstantinos Mavropanos da kuma Hector Bellerin dukannin su sakamakon rauni.
Sai dai ana sa ran likitocin kungiyar ta Arsenal za su auna dan wasanta Nacho Monreal ko zai iya buga wasan, inda ake sa ran cewar Shkodran Mustafi zai dawo filin atisaye a wannan makon.
A gefe guda kuwa, rahotanni na nuna cewar dan wasanta Henrikh Mkhitaryan zai tafi jinya har na tsawon sati shida, inda aka bayyana Danny Welbeck da cewar za iya daukan tsawon lokaci kafin ya dawo filin taka leda.
Don haka Kungiyar ta na fama da rashin 'yan wasa a yanzu haka, Arsenal dai tana matsayi na 5 ne a saman teburin firimiya lig mako na 18, da maki 37 dai dai da Chelsea wace take matsayi na 4, a ranar Asabar ne Arsenal ta lallasa Burnley daci 2-1.
Facebook Forum