A rahoton duba zaben, kungiyar ta ja hankalin hukumar zabe game da irin matsalolin da aka fuskanta a lokacin zabe, kamar rashin isar kayan aiki mazabu, rashin fara aikin zabe a kan lokaci, matsalar na'urar tantancewa da kuma rashin isashshen horo ga masu aikin gudanar da zaben.
Rev. Dr. Yusuf Ibrahim Wushishi, sakataren kungiyar, da Dr. Simon A.S Dolly, babban daraktan tattaunawa tsakanin addinai a Abuja sun ja hankalin matasa game da bangar siyasa musamman bayan zabe.
A hirarta da Sashen Hausa, Rachael John, daga jihar Kaduna tace duba zaben abune mai muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a kasa.
Dama dai kungiyoyi masu zaman kansu dana addinai su kan duba yadda babban zabe ku gudana da, kuma fitar da rahoto kan shawarar su da nufin ganin an sami inganci a lokuta na gaba.
Wakiliyar sashen Hausa a birnin Tarayya Abuja, Hauwa Umar ta aiko muna da wannan rahoton.
Facebook Forum