Kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, dake tarayyar Najeriya Ibrahim A Musa, ya bayyana jin da dinsa bisa nasarar da suka samu a wasan mako na 7, cikin gasar Firimiya lig Najeriya na shekarar 2019/20.
Ibrahim ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labarai, jim kadan bayan kammala wasan da su kayi da Delta Force inda suka lallasa ta da ci 6-1, a filin wasa na tunawa da marigayi Sani Abacha dake kofar mata a Kano ranar Lahadi.
Ibrahim ya fara da mika godiya ga Allah, ya kara da cewar halin da Kano Pillars ta tsinci kanta a baya na rashin nasara wata jarabawa ce, amma idan aka yi hakuri komai zai wuce, kuma ga shi an fara samun nasara musamman a wasan da su kayi kwanakin baya da Plateau United, inda suka yi canjaros 0-0, da kuma wasan su da Akwa Starlent har gida suka doke su da 2-1.
A makonnin da suka gabata, farkon gasar kungiyar Lobi ta doke Kano Pillars a gida, sai kuma Wikki tayi canjaras da ita 0-0.
Da wadannan nasarorin da Kano Pillars ta samu yanzu haka tana matsayi na 10 a teburin mako na 7 a gasar firimiyar bana da maki Tara.
A ranar Lahadi mai zuwa za tayi tattaki zuwa jihar Nasarawa domin fafatawa da Nasarawa United a wasan mako na takwas.
Facebook Forum