Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Jibwis Ta Yi Babban Taron Addu’a A Abuja


Shugaban Kungiyar Jibwis Imam Abdullahi Bala Lau
Shugaban Kungiyar Jibwis Imam Abdullahi Bala Lau

Malaman Islama sunyi gagarumin taron addu’a a babban birnin Najeriya, Abuja, don neman jagorar Allah ga gwamnatin kasar ta ‘kara nasara a lamuran tsaro da suka hada da kwato ‘yan matan Chibok da sauran mutanen da ke hannun ‘yan ta’adda.

Malaman da suka jagoranci taron sun hada da shugaban JIBWIS, Imam Abdullahi Bala Lau, wanda yace an tsara ci gaba da wannan addu’ar duk bayan kwana 100 don neman taimakon Allah ga nasarar gwamnatin Najeriya ta samu damar farfado da tattalin arziki da magance cin hanci da rashawa da kuma ‘kara inganta lamuran tsaro.

Imam Abdullahi Bala Lau, ya bukaci jama’ar Najeriya su koma ga Allah, don samun nasara maimakon daura alhakin durkushewar tattalin arziki ga gwamnati. Malamin ya bukaci shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da ya ci gaba da tsayawa kan adalci da amana, haka kuma da amfani da hanyoyin samun bayanai don sanin halin da kasa ke ciki.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-HIkaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG