Kungiyar JIBWIS a Najeriya zata yi anfani da watan Ramadan na bana wajen yaki da shan miyagun kwayoyi da ya ta’azzara tsakanin matasan Najeriya.
Shugaban kungiyar Shakih Abdullahi Bala Lau shi ya bayyana hakan a taron bita ga malamai akan al’amuran da zasu wakana a lokacin tafsirin azumin bana. Haka ma an yiwa ‘yan aikin agajin kungiyar bitar akan dabarun aikin jin kai.
A jawabinsa Shakih Abdullahi Bala Lau ya ce wasu alkalumma da aka fitar sun nuna akwai matasa miliyan 14 dake shan kwayoyi a Najeriya kuma miliyan 12 daga cikinsu daga arewacin Najeriya suka fito. Ya jaddadawa matasa anfanin samun ilimin addini da na zamani, wadanda ya ce zasu taimaka wajen fitar da al’umma daga kangin talauci da wahala. Ya gargadi matasa kada su zama ‘yan bangan siyasa amma su yi ilimi su kuma shiga siyasa.
Bako mai jawabi Farfesa Aliyu Bunza, yace al’ummar da bata da ‘yan agaji ta zama abun tausayi. Shi ma daraktan agaji na kungiyar Injiniya Imam ya tabbatar wa kungiyar agaji, samun hadin kan jami’an tsaro.
Duk ‘yan aikin bada agaji na kungiyar, ‘yan aikin sa kai ne. Babu wanda yake karbar albashi ko wani alawus.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum