Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Sare Kawunan Wasu 'Yan kasar Masar


Shugaban kasar Masar El-Sissi
Shugaban kasar Masar El-Sissi

Kasar Masar ta kai hari akan kungiyar ISIS cikin Libya a zaman martani kan kashe 'yan kasarta da kungiyar tayi.

Masar ta kai wani farmaki da jiragen yaki a gabashin Libya jiya Litinin, a wani matakin ramuwar gayya ba tareda wani bata lokaci ba, saboda kisan gillar da aka yiwa kiristoci 'yan kasar Masar mabiya darikar koptic, da 'yan kunigyar ISIS a Libya suka aiwatar.

Masar ta kashe mayakan sakai masu yawa harda ma wasu fararen hula a harin na bama-bamai da ta kai, kan garin da ake kira Darna, inda aka hakikance nan ne tungar mayakan sakan, kamar yadda jami'an kasar suka yi bayani. Garin yana da tazarar kilomita 1,300 gabas daga wurin da inda aka kashe mutanen.

A jawabin da yayi ta talabijin, shugaban Masar Abdel Fattah el-Sissi, yayi alkawarin mai da martani ga kisan da ya kira "mummunan ta'addanci". Mr. Sissi yace "Masar tana da 'yancin ta maida martani, kuma kan hanyar da a ganinta da kuma lokaci da ta zaba, kan wadannan 'yan kisan kai, baragurbi,wadanda basu da wata siga ta mutanen kwarai".

Tareda goyon bayan mayakan saman Libya, karkashin gwamnatin kasar wacce take samun goyon bayan hukumomin kasa- da-kasa, a harin an auna rumbun makamai, da kuma sansanonin horaswa.

Kishiyar majalisar dokokin kasar wacce take Tripoli wacce mayakan sakan suke goyon baya, sunyi Allah wadai da hare haren, suna cewa hakan ya kaucewa dokokin kasa -da kasa, da diyaucin Libya.

Masar ta fara daukar wannan matakin ne bayan da aka nuna wani fefen vidiyo a internet jiya Lahadi inda aka nuna hotunan yadda aka datse kawunan wasu mutane maza,wadanda aka kama ana garkuwa dasu a Libya a cikin watannin baya bayan nan, bayan da aka ware su daga sauran abokan ayyukansu musulmi.

Har yanzu babu tabbas na lokacin da aka aiwatar da kisa kan mutanen. Wadannan kuma su ne mutane masu yawa haka, wadanda kungiyar ISIS ta hallaka a wani wuri ba Syria ko Iraqi da kungiyar ta yayata ba.

XS
SM
MD
LG