Jami'an Amurka sun ce babu alamun cewarsatar shiga na'urorin komputocinta ne mayakan sakai na ISIS suka saci bayanai kan wasu sojojinta 100 da suka hada da hotunansu da adireshinsu da suka saka a internet, kuma suka nemi magoya bayan kungiyar da suke Amurka su kashe su.
Wani jami'in tsaro na Amurka ya gayawa Muryar Amurka cewa "babban burinsu shine tabbatar da lafiyar dakarunta, daga nan yayi kira ga sojojin Amurka su dauki matakan tsaro na musamman da aikinsu ya tsara. Ya kara da cewa duka rundunonin suna da matakai na tuntuba kamar yadda ka'idojinsu suka tsara". Yace ma'aikatar tsaron Amurka tana daukar duk barazana da aka yi mata da muhimmancin gaske.
Da aka tambayi jami'in ko ana iya samun bayanai da kungiyar ISIS ta wallafa kan sojojin a internet kawai, yace kwarai kuwa, misali ta shiga dandalin Facebook inda za'a iya samun bayanai sosai.
Gungun wadansu da suka kira kansu sashen masu satar shiga komputoci na ISIS, ranar Lahadi tace bayanan sojojin da tace suna cikin dakarun Amurka da suke kai farmaki ta sama kan muradun ISIS a Iraqi da Syria, sun samo bayanan ne daga komputocin gwamnatin Amurka.
Amma wani jami'in tsaro na Amurka yace babu alamun mayakan sakan sun saci shiga na'uorrin Amurka ne suka samu wadannan bayanan.