Bayan an jima ana jiran cika alkawarin da kungiyar gwamnonin tayi sai gashi ta fara bada nera miliyan 34 cikin 100 din da tace zata bayar.
Sakatariyar gwamnatin jihar Nasarawa Hajiya Zainab Ahmad ta yabawa kungiyar gwamnonin da kudin da ta bayar ta kuma roki gwamnonin su karasa cika alkawarin da suka dauka.
Hajiya Zainab tace sun raba kudin daidai-wadeta inda kowace mace ta samu nera 490,000 da 'yan kai. Yayin da take raba kudin tace sun rasa 'yansanda guda 64 da 'yansandan dake saka fararen kaya ko SSS 10, wato an yi asarar jami'an tsaro 74 a kwantar baunar da kungiyar Mbatse ta kabilar Eggon tayi masu.
Tun can farko jihar Nasarawa ta ba kowanensu tallafin nera miliyan daya daya. Mataimakin kwamishanan 'yansandan an baiwa matarsa nera miliyan biyar a matsayin taimako. Ban da haka matar gwamnan jihar ta ziyarci matan a Akwanga inda suke zaune domin nan ne mazaunin 'yansandan kwantar da tarzoma.
Gwamnonin basu fadi lokacin da zasu biya sauran kudin ba kimanin nema miliyan 64 amma Hajiya Zainab tace suna kawowa za'a sake rabawa matan da iyalansu.
Kakakin matan da suka rasa mazansu Madam Afiniki Daniel bata yadda a yi mata tambaya ba a kan kudaden da aka basu.
Ga rahoton Zainab Babaji.