Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sallami mai horas da 'yan wasan ta Marco Silva, bayan ya kwashe watanni 18 ya na jan ragamar kungiyar.
Marco Silva, dan shekaru 42 da haihuwa, ya kama aiki ne a watan Mayun shekarar 2018, inda ya jagoranci wasanni 60 a kulob din, yayi nasara a wasanni 24, ya kuma baras da wasanni 24, kana sai kunnen doki 12.
A ranar Larabar da ta gabata Liverpool ta lallasata da kwallaye 5-2 cikin gasar Firimiya lig na Ingila wasan mako na 18, inda yanzu take matsayi na 18 a teburin bana da maki 14.
Kungiyar ta bayyana dalilin sallamarsa ne sakamakon rashin tabuka abun kirki.
Tuni dai kungiyar ta ayyana tsohon dan wasan gaban nan Duncan Ferguson, amatsyin wanda zai maye gurbin Silva, zai kuma fara aiki na farko da jan ragamar wasan sa na ranar Asabar tsakanin Everton da Chelsea.
Hukumomin kulob din sunce suna da niyar nada sabon kocin na din-din-din nan bada jumawa ba, wanda zai kasance na hudu a jerin masu horas da 'yan wasanta da ta sallama tun daga kan Roberto Martinez, wanda ta sallame shi a shekarar 2016.
Silva, ya kasance mai horas da 'yan wasa cikon na biyar kenan da aka sallama a kungiyoyi daban-daban, dake kasar Ingila a bana masu buga wasan firimiya lig, wanda suka hada da Javi Gracia Quique, Sanchez Flores daga Watford, da kuma kocin Tottenham Mauricio Pochettino, sai na Arsenal Unai Emery.
Facebook Forum