Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Mali


Tsohon shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure
Tsohon shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure

Shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure ya yi murabusa daga mukaminshi, makonni bayanda sojoji suka hambare gwamnatinshi.

Shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure ya yi murabusa daga mukaminshi, makonni bayanda sojoji suka hambare gwamnatinshi, ana sauran ‘yan watanni wa’adin mulkinshi ya cika.

Mai shiga tsakani na kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika- ECOWAS, yace ya sami wasikar murabus na Mr. Toure jiya Lahadi.

Wani jami’in ECOWAS ya shaidawa Muryar Amurka cewa, kungiyar ta dage zazzafan takunkumin tattalin arzikin da ta kakabawa kasar Mali, da cewar ta gamsu da amincewa da rundunar sojojin ta yi na amfani da kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai jami’in yace, zai zama da hadari idan sojojin suka karya alkawarsinsu na gudanar da zabe karkashin tsarin damokaradiya. Yace bai ga yadda kasar dake kungiyar ECOWAS zata maida kanta saniyar ware ba.

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma ranar jumma’a, tsohon kakakin majalisa Dioncounda Traore zai rike mukamin shugaban kasa karkashin gwamnatin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.

Kungiyar ECOWAS ta yi alkawarin taimakawa kasar Mali wajen yakar ‘yan tawayen azbinawa da suka kwace ikon galibin arewacin kasar, suka kuma ayyana ‘yancin kai a yankin bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Shugabannin juyin mulkin sun bayyana cewa, sun hambare gwamnatin ne sabili da ta gaza shawo kan tada kayar bayan da arbinawa ke yi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG