Sakataren kungiyar ta kasa Danladi Garba Fasali yace sun samu lasisi kuma sun samu filayen da zasu gina matatun a jihohin Bayelsa da Kogi. Tuni sun kira wasu kwararru daga kasashen waje har sun duba wuraren. Gwamnati ma ta yadda ta yi sassauci.
Maimakon gwamnati ta dinga ba masu shigo da tacaccan mai tallafi kamata yayi a ba wadanda zasu tace a cikin kasar tallafi wanda kuma gwamnati ta yadda da hakan. Idan aka kafa matatun za'a iya daukan akalla mutane miliyan daya aiki.
Za'a gina matatun da hadin gwiwar masu saka jari daga waje. 'Yan kasuwa daga Ingila sun taru sun hada hannu su zuba jarin dalar Amurka biliyan uku. Su kuma 'yan Najeriya da kungiyar dillalan man fetur zasu saka kashi 60 cikin dari na kudaden da ake bukata ko kuma dalar Amurka biliyan bakwai da miliyan dari biyar.
Sabili da karancin wutar lantarki a Najeriya matatun zasu tanadi nasu wutar da zasu yi anfani da ita.
Ga cikakken bayani na Medina Dauda.