WASHINGTON, D.C. —
A yayin da aka bude hada hadar cinikaiyan 'yan wasan kwallon kafa na duniya a watan Janairu 2019, kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala cinikin dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund mai suna Christian Pulisic, akan kudi fam miliyan £58.
Dan wasan mai shekaru 20 da haihuwa dan kasar Amurka, wanda a da ake alakantashi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, ko Arsenal, ya shiga tawagar Borussia Dortmund ne a shekara ta 2015 alokacin yana matashi.
Chelsea ta amince da ta bada shi aro ga kungiyarsa ta Dortmund, bayan da ta biya kudin sa inda zai cigaba da taka leda har zuwa karshen kakar wasan bana.
Dan wasan ya taka leda wa kasarsa ta Amurka wasanni 23 inda ya samu nasarar jefa mata kwallaye 9.
Facebook Forum