Wannan ne dai kusan karo na uku a kasa da mako guda da yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a wasu kauyuka na yankin Madagalin dake daura da dajin Sambisa.
Yayin wannan harin ,kamar yadda rahotanni ke cewa yan tada kayar bayan sun yi shigar burtu ne a kauyen Bakin Dutse a wani yanayi na masu makoki,da hakan ya jawo hankalin jama’a zuwa inda suke wanda kuma nan take suka soma bude wuta ba kakkautawa.
Kawo yanzu hukumomin tsaro basu yi karin haske ba tukunna game da wannan sabon harin.
To sai dai dan majalisar wakilai mai wakiltar Madagali da Michika,Mr Adamu Kamale,ya tabbatar da faruwan lamarin,inda ya bukaci da a kara tura sojoji zuwa wasu yankunan dake kusa da dajin na Sambisa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da wa’adin da babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya dibarwa dakarun sojin kasar na su kamo Imam Abubakar Shekau dake zama shugaban wani bangaren na kungiyar Boko Haram ke kara karadowa,batun da masana harkar tsaro ke ganin akwai abun dubawa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum