Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Shabab Ta kashe Mutane Da Dama A Wani Mummunan Hari A Ranar Juma'a


Somalia Hotel Attack
Somalia Hotel Attack

An kashe akalla mutane 32 kana wasu 63 sun jikata bayan wani hari da kungiyar al-Shabab ta kai a wani wurin mai cunkoson jama’a na bakin teku a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia da yammacin jiya Juma’a, a cewar kakakin ‘yan sandan Somalia, Manjo Abdifatah Aden Hassan.

Harin ya fara ne da misalin karfe 10 na dare agogon yankin, yayin da wani dan kunar bakin wake ya tada bam a wurin shakatawa na gabar teku mai yawan jama’a da suka je shakatawan dare.

Wasu hotunan bidiyo da aka kafe a yanar gizo daga wurin sun nuna mutane da dama kwankwance, wasu sun mutu wasu kuma sun samu munanan raunuka.

Bayan fashewar farkon, wasu ‘yan bindigan al-Shabab uku sun kai samame a dakin cin abinci da nishadi na bakin tekun.

Bugu da kari bayan kashe fararen hular, jami’an tsaro dake wurin sun kashe maharan, a cewar ‘yan sanda. Wani dan bindiga na hudu ya tarwatsa kansa, a cewar rahoto.

Nan da nan gwamnatin Somalia ta jibge rundunar tsaro domin fafatawa da maharan, a cewar shedu. Jami’an tsaron sun shaidawa ma’aikatar labaran kasar cewa sun dakile lamarin sa’o’I hudu bayan harin.

Asibitoci a Mogadishu sun yi kira ga taimakon jini domin ceto rayuwar mutanen da aka raunata a harin.

Al-Shabab ta saba kai hari a gidajen cin abinci da otal a bakin tekun Lido tsawon shekaru saboda wuri ne iyalai suka fi sha’awa, da matasa da ma mazauna kasashen waje da ke dawowa gida don yin cudanya da juna.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG