Erik ten Hag, mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Ajax, ya bayyana cewa kungiyoyin kwallon kafar Real Madrid da Juventus duk sun nuna tsoronsu a wasannin da Ajax ta dokesu a gida, a gasar cin kofin zakarun turai "UEFA Champion League", na bana.
Ajax ta yi waje da Real Madrid cikin wasan zagaye na biyu a gasar ta UEFA, Real Madrid dai ita ce take rike da kambun.
Ajax ta sake bada mamaki a duniya, inda ta sake samun nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ci 2-1 har gidanta, hakan ya sanya ta kawo karshen burin Juventus na lashe gasar ta bana.
Ajax, wacce ta taba lashe gasar cin kofin na zakarun turai har sau hudu a tarihi, ta samu zuwa matakin wasan kusa dana karshe a karon farko tun bayan shekara 1997, kimanin shekara 22 kenan da suka gabata wanda wannan ba karamin tarihi bane ga kungiyar da kuma kasar Holland gaba daya.
Kamar yadda kocin ya bayyana cewar, mun samu nasarar fitar da wasu manyan daga cikin kungiyoyin da ake tunanin zasu iya lashe wannan gasar.
Bayan haka kuma mun wuce matakin da ake zaton zamu iya kaiwa a kakar ta bana, saboda haka duk abin da mukayi yanzu kawai riba ce a garemu da muke samu.
A yanzu haka kungiyar ta Ajax za ta kara da Tottenham ne a matakin wasan daf da na karshe "Semi final" cikin gasar cin kofin zakarun Turai sai kuma Barcelona ta karbi bakuncin Liverpool na kasar Ingila. Za'a fafata wasannin ranar 30 ga watan Afirilu 2019.
Facebook Forum