Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun kolin Amurka yace Iran zata biya diyar dala biliyan biyu


Ginin kotun kolin Amurka
Ginin kotun kolin Amurka

Kotun kolin Amurka tace dole kasar Iran ta biya akalla Dalar Amurka biliyan 2 ga iyalan Amurkawan da suka mutu sakamakon ayyukan ta’addancin da gwamantin Tehran ta tallafawa. Ta hanyar biyan kudin daga kaddarorin Iran da aka dakatar a nan Amurka.

A hukuncin Kotun na jiya Laraba, ta yi amfani da dokar yadda ake kasafta dukiya, wacce ta ce za’a biya diyya ga iyalan sojojin ruwan Amurka guda 241 da aka hallaka a harin ta’addancin shekarar 1983 a birnin Beruit na kasar Lebanon.

Sai kuma wasunsu da suka mutu a harin shekarar 1996 akan tagwayen tulluwar Khobar a Saudiyya, dama wasu hare-hare makamantansu. Hukuncin da kotun ta yanke don yin adalci ga iyalan sojojin da suka mutu a wadannan hari da Iran ta dau nauyinsa.

Hukuncin da ita Iran ta nuna rashin amincewa da shi, wanda tuni Lauyoyin wadanda abin ya shafa suka bazama neman duk inda wata kadarar kasar ta Farisa ta ke a nan Amurka don kaiwa gareta.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka dai a jiya Laraba ta ce yanke hukuncin bai zo mata da bazata ba, kasancewar dama tuntuni gwamanti ta nuna goyon bayan maganar biyan diyyar ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG