Wata kotu a Kenya ta yi watsi da karar da ke kalubalantar matakin da gwamnatin kasar ta dauka na dage haramcin shiga da abincin da aka shuka ta hanyar amfani da kimiyya ko kuma wadanda aka sauya wa yanayi – wato nau’in abincin da aka fi sani da GMO a turance.
Gamayyar kungiyar lauyoyin Kenya ne suka shigar da karar, inda suka yi korafin cewa irin wannan nau’in abinci na iya yin illa ga lafiyar jama’a.
Lauyoyin sun kara da cewa dage haramcin shiga da shi kasar da gwmnati ta yi ya saba wa doka.
Sai dai yayin yanke hukunci a karshen makon nan, babbar kotun Kenya karkashin mai shari’a Oscar Angote, ta ce kungiyar lauyoyin, sun gaza gabatar da hujjojin da ke nuna cewa abinci na iya illa ga lafiyar jama’a.
A watan Oktoban bara gwamnatin ta Kenya ta dage haramcin shiga da nau’in abincin da aka sarrafa shi ta hanyar fasahar kimiyya saboda barazanar matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta da kuma gazaw da manoman kasar suka yi wajen noma abincin da zai ishi al’umar Kenya.
Dandalin Mu Tattauna