Kotun kasa da kasa ICC ta baiwa masu shigar da kara wa'adin mako daya, su karfafa karar da suka shigar kan shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ko kuma su yi watsi da ita.
An sha dage wannan shari'ar, kuma a jiya Laraba kotun ICC dake Hague kasar Holland ko Netherlands ta gabatar da sanarwar tana mai cewa jinkirtawa da ake yi zai zama rashin adalci ga shari'a.
Mr.Kenyatta yana fuskantar caje cajen laifuffukan cin mutuncin Bil Adama bisa zargin cewa shine ya kitsa tarzomar bayan zaben da ta kashe kimamin mutane dubu daya a kasar Kenya a karshen shekarar dubu biyu da bakwai zuwa farkon shekarar dubu biyu da takwas Tarzomar ce kuma tayi sanadiyar da fiye da mutane rabin miliyan suka rasa matsuguninsu.
Mr.Kenyatta ya ce bai aikata laifin ba.
Lauyoyi sunce karar ta ruguje, amma masu shigar da kara sun ce gwamnatin kasar Kenya ce tasa kafar angulu ga yunkurin tattara shedu da bayanai i.