Alkalai a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, da ke Hague, sun wanke tsohon mataimakin shugaban kasar Congo, kuma tsohon shugaban 'yan tawaye Jean- Pierre Bemba, daga laifukan yaki da aka sami dakarunsa da aikatawa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
A jiya juma’a, Kotun daukaka karar ta wanke hukuncin shekaru 18 da aka yankewa Bemba, a hukuncin da mai shari'a Christine Van den ta jagoranta, inda ta ce babu yadda za a kama shi Bemba da laifin da dakarunsa suka aikata a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Wannan sabon babi da shari’ar ta bude, babban koma baya ne ga masu shigar da kara a kotun ta hukunta manyan laifuka, wadanda suka jajirce cewa, za a iya kama kwamanda kan laifukan da dakarunsa suka aikata, saboda ya gaza hana su ko kuma ya hukunta su dalilin laifukan da suka aikata.
Har ila yau, wannan sabon hukunci ka iya shafar sauran shari’o’in da ake yi, na kokarin gurfanar da kwamandoji da dakarunsu suka aikata laifukan yaki.
A baya an samu Bemba da laifin aikata laifukan yaki da suka hada da kisa da fyade da dakarunsa suka aikata a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a tsakanin shekarun 2002- 2003.
Facebook Forum