Bayan wankewar da kotun da'ar ma'aikatan ta yiwa Saraki bisa zargin laifuffuka goma sha uku, sai kuma gwamnati ta sake maka shi a kotun daukaka kara bisa rashin gamsuwa, wacce ita kuma kotun ta umarci Malam Saraki da ya koma kotun ta Da'ar Ma'aikatan don sake amsa batun wasu zargin laifuffukan guda uku.
A hukumcinta kotun ta wakenshi daga laifukan lamarin da ya sa gwamnatin tarayya ta garzaya kotun daukaka kara wacce yanzu ta ce shi Dr. Saraki ya koma kotun da'ar ma'aikatan ya fuskanci zargi uku.
Kotun daukaka kara tace shugaban Majalisar Dattawa ya koma kotun da'ar ma'aikata domin ya amsa tuhumar da ake yi masa. Dama can ana tuhumarsa da aikata laifuffuka goma sha takwas ne, amma kotun daukaka kara tace a yi watsi da guda goma sha biyar ayi anfani da guda uku kacal a wajen tuhumarsa.
Batutuwan uku da za'a yi masa shari'a akai sun hada da batun sayen gidajen da Dr. Sarakin yace ya saya a Lagos lokacin da yake gwamnan Jihar Kwara. Don jin ko ana iya sake tuhumar mutum bayan kotu ta wanke shi ko a'a, Barrister Mainasara Kogo Ibrahim ya yiwa Muryar Amurka bayani.
Inda yace, mayar da karar zuwa kotun Da'ar Ma'aikata alheri ne, domin da bata mayar da batun ba to da shi kenan Dakta Bukola ya tsira. A cewarsa, dokar da ta kafa kotun, ta bada damar a sake gurfanar da mutum, musamman ma akan abin da ya shafi laifuffukan kasa.
Sannan idan kotun ta sami mutum da laifi tana iya cireshi daga kan kowane mukami yake rike da shi, tare da hanashi sake rike wani mukami har na tsawon shekaru goma.
Kwararru masu fashin baki akan al'amuran yau da kullum irin su Abdulrahaman Abu Hamisu, sun yi tsokaci akan matakin da kotun daukaka karar ta dauka. Inda yace, duk wanda ya ke son dimukuradiyya da zaman lafiya, da ci gaban kasa, to yayi na'am da wannan matakin da kotun daukaka karar ta dauka.
Ga cikakken rahoton Wakiliyarmu Medina Dauda.
Facebook Forum