Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu ta Yankewa Wani Ba'amarike Hukuncin Daurin Shekara 21 Domin Kasancewarsa Dan al-Qaida


 Eric Holder Sakataren Ma'aikatar Shari'ar Amurka
Eric Holder Sakataren Ma'aikatar Shari'ar Amurka

Wani alkali ya karawa wani ba'amarike karin wa'adin da zai zauna gidan kaso domin an sameshi da laifin kasancewa dan kungiyar al-Qaida

Wani ba Amurke Jose Padilla da kotu ta samu da laifin goyon bayan kungiyar al-Qaida, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru 17 an kara masa shekaru hudu, domin wani alkali ya yanke hukunci jiya talata cewa an yi masa sassauci ainun.

Padilla dan shekaru 43 da haifuwa, wanda aka sameshi da laifi a 2007 a shari’ar da aka yi masa a jihar Florida dake kudancin Amurka, an kama shi ne a 2002 a tashar saukar jiragen sama dake Chicago, bayanda ya dawo Amurka daga abunda masu gabatar da kara suka kira sasanin horaswa na kungiyar al-Qaida a Afghanistan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG