Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tabbatar Da Zaben Buhari


Buhari second inauguration
Buhari second inauguration

Bayan zaman sama da sa’oi bakwai Kotu tayi watsi da karar da jam’iyar PDP da dan takarar shugaban kasarta Atiku Abubakar suka shigar suna kalubalantar sake zaben shugaba Muhammadu Buhari.

Kotun ta bayyana cewa, babu wata shaida da ta nuna cewa hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yayata sakamakon zaben ta hanyar sadarwar internet.

Da yake sanar da hukumcin kotun, shugaban kotun ta musamman Alkali Mohammed Garba yace dan takarar shugaban kasar na Jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya gaza gabatar da cikakkar hujjar cewa hukumar zaben tayi amfani da na’urar comfuta wajen fitar da sakamakon zaben

Da yake maida martani jim kadan bayan yanke hukumcin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace nasarar da ya samu a kutun sauraron karar, nasara ce ga Najeriya baki daya, ya kuma bayyana cewa, gabanshi bai taba faduwa ba duk tsawon lokacin da aka dauka ana sauraron karar kasancewa shine ‘yan Najeriya suka zaba.

Shugaba Buhari ya yabawa fannin sharia da yace ya gudanar da aikinsa ba sani ba sabo, ya kuma ce yanzu lokaci ne da ya kamata a maida hankali wajen yi wa kasa aiki.

Tuni jam’iyar PDP tayi watsi da hukumcin da kotun ta yanke da ta bayyana a matsayin rena tsarin sharia.

Ku ci gaba da ziyartar shafin namu domin samun karin bayani kan wannan hukumcin.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG