Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KOTU: Muhammad Alkali Na PRP Ne Ya Lashe Zaben Majalisar Wakilai Ta Bassa/Jos-Arewa


Gwani Muhammad Adam Alkali
Gwani Muhammad Adam Alkali

Kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Filato ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta ayyana Muhammad Adam Alkali na jami'iyyar PRP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta Jos ta Arewa da Bassa.

Tun farko dai hukumar zaben ta ayyana Musa Avia Agah na jami'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a farkon wannan shekarar ta 2022.

Muhammad Adam Alkali na jami'iyyar PRP, wanda shi ma ya tsaya takarar kujerar ya shigar da kara a kotu don kalubalantar sakamakon zaben.

Kotun sauraren kararrakin zabe ta ce ta gano an yi aringizon kuri'u a yankin Tudun Wada, Kabong da wasu sassan karamar hukumar Bassa.

Kotun ta ce bayan tantance rahoton zaben da na'urar BVAS, ta gano cewa an kara wa Musa Avia Agah na PDP kuri'u dubu goma sha uku, abinda ya sa hukumar zaben ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.

Jam’iyyun siyasa 11 ne dai suka fafata a zaben maye gurbin da aka yi ranar 26 ga watan Fabrairu domin cike gurbin da Haruna Maitalla na jam’iyyar APC wanda ya rasu a wani hatsarin mota a watan Afrilun shekarar 2021 ya bari.

XS
SM
MD
LG