Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Ce Sabon Makaminta Na Iya Auna Pacific


Wani makami mai linzami na Koriya Ta Arewa samfurin hypersonic
Wani makami mai linzami na Koriya Ta Arewa samfurin hypersonic

Koriya Ta Arewa ta sake gargadi game da ingancin sabbin makamanta.

Koriya ta Arewa ta ce gwajin makamin da ta yi na baya-bayan nan ya hada da wani sabon makami mai linzami mai cin dogon zango da aka kera domin kai hari a yankin tekun Pasifik a daidai lokacin da shugaba Kim Jong Un ya sha alwashin kara fadada aikin kera makaman nukiliyar da ya ke yi.

Koriya ta Arewa ta bayyana nau'ukan makamai masu yawa a bara, ciki har da makamai masu linzami masu cin dogon zango, wadanda za ta iya kai hari da su a makwabciyarta Koriya ta kuda da Amurka, sannan akwai fargabar cewa karfin sojanta na iya karuwa yayin da take amfani da fasahohin Rasha, bayan da kasashen biyu suka zama abokai a yakin da Rasha take yi da Ukraine.

Kim ya sake nanata cewa yunkurin kera nasa makaman nukiliya don tinkarar barazanar da kasarsa take fuskanta ne amma bai ambaci Amurka kai tsaye ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG