Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kogi: Bayan Zabe Ku Tsaya A Kirga Kuri'unku - Osinbajo


Farfasa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa
Farfasa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya kasance a gangamin karshe na neman kujerar gwamnan jihar Kogi da dan takarar APC Abubakar Audu ya gudanar a Lokoja fadar gwamnatin jihar

Yanzu dai aski ya zo gaban goshi game da zaben gwamnan jihar Kogi da za'a gudanar jibi Asabar idan Allah Ya kaimu..

'Yan takara kimanin ashirin daga jam'iyyu daban zasu fafata amma 'yan takarar jam'iyyun PDP da APC ke kan gaba.

Jiya Laba Prince Abubakar Audu na APC ya gudanar da gangamin neman zabe na karshe inda mataimakin shugaban kasa ya kasance.

Yayinda mataimakin shugaban kasa wato Farfasa Yemi Osinbajo yake jawabi a wajen gangamin yace "bayan kun gama kada kuri'unku to ku tsaya wurin har sai an kirga kuri'un an kuma baku sakamako".

Magoya bayan APC sun ce suna da kwarin gwuiwar samun nasarar karbe kujerar gwamna daga hannun Idris Wada na PDP. Onarebul Adamu Modibo Umar shugaban APC a jihar yace kwarin gwuiwarsu ya ta'allaka ne akan alherun da Prince Audu ya yiwa jama'a can baya.

A bangaren PDP Onarebul Alhassan Tunduwa yace suna jiran lokaci ne kawai. Kuma taron APCin baya tada masu hankali domin 'yan cin kasuwa APC ta tara daga wasu jihohin. 'Yan karen farauta ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG