Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan ya yi gargadi game da kara makamai da sojoji a kasar Sham


Kofi Annan
Kofi Annan

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Sham Kofi Annan, yace kara makamai ko sojoji a kasar ba zai haifar da komai ba sai dada munin halin da ake ciki.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen larabawa na musamman a kasar Sham, Kofi Annan, yace kara makamai ko sojoji a kasar ba zai haifar da komai ba sai dada munin halin da ake ciki.

Mr. Annan ya bayyana wannan yau alhamis a al-Qahira, inda ya gana da sakatare janar na kungiyar kasashen larabawa, Nabil el-Arabi. Tsohon babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya zai ziyarci kasar Sham a cikin wannan makon.

A halin da ake ciki, mukaddashin ministan mai na Sham yayi murabus daga kan mukaminsa ya shiga cikin gungun masu yin adawa da shugaba Bashar al-Assad, yana mai fadin cewa gwamnati ta haddasa bakin ciki da alhini na tsawon shekara guda kan al’ummar kasar.

Shi ne jami’I mafi girma da ya taba canja sheka daga gwamnatin Sham zuwa ga bangaren ‘yan adawa tun fara tunzurin watan Maris na bara. Shugaban majalisar kasa ta ‘yan adawar Sham yayi marhabin da wannan canjin sheka, ya kuma yi kira ga sauran jami’ai da su bi sahu.

A yau alhamis a birnin Damascus kuma, babbar jami’ar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, Valerie Amos, ta gana da jami’ai a ma’aikatar al’adu, ana kuma sa ran zata gana da wakilan hukumomin ayyukan jinkai.

Ta ce ta ziyarci tungar ‘yan adawa a birnin Homs jiya laraba, kuma ta ga wasu sassan unguwar sun zamo kango. Amos da wakilan kungiyar agaji ta Red Crescent sun ziyarci Baba Amr na tsawon mintoci 45. Kakakinta ta ce sun yi kokarin shiga yankunan dake hannun ‘yan adawa a unguwar, amma ‘yan adawar sun hana su shiga ciki.

XS
SM
MD
LG