Kocin kungiyar kwallon kafa ta tawagar Matan Najeriya Super Falcons Thomas Dennerby ya ajiye aikinsa.
Thomas dan shekaru 66 da haihuwa, dan asalin kasar Sweden wanda ya jagoranci tawagar Matan suka lashe gasar cin kofin na Matan Afirka AWCON, a shekarar sa ta farko da kama aiki, ya bayyana ajiye aikin nasa ne bisa dalilin rashin biyansa kudin Albashinsa, da kuma rashin samun hadin kai daga hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya wato NFF.
Rahotanni dangane da labarin na nuna cewar Kocin Dennerby ya aike da wasikane zuwa ga hukumar NFF, kan ajiye aikin nasa kafin wannan lokacin kungiyar ta Super Falcons ta buga wasanni guda biyu ba tare da kocin ba.
Haka kuma baya cikin tawagar kungiyar wacce ta kasance sau 8 tana zamowa zakara a nahiyar Afrika a gasar AWCON, a bana kuma bata samu tikitin zuwa wasannin motsa jiki na duniya Olympic da za ayi a Tokyo 2022, bayan da Ivory Coast ta cireta.
Kocin yana da sauran shekara guda ya kammala yarjejiniyar kwantirakinsa da hukumar ta NFF, yace ya bar komai a hanun lauyansa.
A wata sanarwa da hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta fitar ta bakin wani jami'inta, lokacin ganawa da 'yan jaridu na kasashen waje, yace ganin takardar ajiye aikin Thomas, bai zo musu da mamaki ba tun watan baya kocin ya yanke shawarar raba gari da Najeriya.
Facebook Forum