Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Unai Emery ya nemi afuwa daga wajan magoya bayan kwallon kafa ta Brighton & Hove Albion, sakamakon kwallo da yayi da Gora a yayin wasansu da sukayi ranar Laraba, da aka tashi kunnen doki 1-1 inda Gorar ta fada cikin magoya bayan kungiyar ta Brighton.
Emery ya bada hakurinne jim kadan bayan an tashi a wasan a wani taro da yayi na manema labarai.
Kocin yace hakan ya farune sakamakon yadda bai ji dadin wasan ba, a wajejen karshen lokacin, shi yasa ya nuna damuwa da fushi har yayi kwallo da gorar wanda ta tsallaka ta samu daya daga cikin magoya bayan kungiyar.
Arsena ta gaza kare kwallo daya da ta jefa tun a farko minti 7 da fara wasan, wadda tabi ta kafar dan wasanta Emerick Aubameyang, daga bisani ana mintuna na 35, dan wasan Brighton Jurgen Locadia, ya farke mata haka dai aka tashi 1-1.
Facebook Forum