An yi wata ganawa a tsakanin Musulmi da Kirista da Turawa a garin Galmi da ke cikin gundumar Malbaza na jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar, domin nunawa duniya cewa ana zaune cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Da suke karbar Musulmin a yayin ziyarar wacce aka kai a jiya Kirsimeti, Pasto Midu Zaku, da Pasto Salisu sun nuna farin cikinsu da ziyarar domin taya su murnar bikin.
Alhaji Shazali hakimin gidan Dutsi, wanda ya yi magana a madadin dukkan hakiman wannan yankin, ya ce sun kai ziyarar zumunci ne.
Musulmin sun nuna farin cikinsu, domin a cewar Liman Nuhu, wannan shi ne ke sawa a kara samun zaman lafiya a cikin kasa.
A nasu bangaren, Kiristocin na Galmi sun nuna jin dadinsu da wannan ziyara ta kasance a tsakaninsu, sabanin zaman doya da man ja da bangarorin biyu ke yi a wadansu kasashe.
Su ma sauran al’umar garin Galmi ‘yan Nijar da turawa sun fada wa wakilin Muryar Amurka cewa, suna jin dadin wannan haduwar tsakanin Musulmi da Kirista a irin wannan locaci.
Ga rahoto cikin sauti.
Facebook Forum