WASHINGTON DC, —
Akasarin kasashen da suka cigaba a duniya, suna amfani da tsarin ajiyar bayanan da suka shafi kasar. Kama daga bayanan al'ummar kasar, har na dabbobi, da kuma kiyasin inda kasar ta dosa.
Kasashen kan tsara abun da suke bukatar cinma a wasu shekaru, inda sukan hasashi dau'ukkan gine-gine da zasu so su gani a kasar, kana bangaren cigaban kimiyya shima sukan bada kaimi wajen ganin an shirya abun da zai faru cikin shekaru masu zuwa.
Kadan daga cikin tattaunawar DandalinVOA da matsahi Bello Isma'il Garkuwa, dalibi dake zurfafa karatu a matakin digiri na biyu a kasar Burtaniya. Don sauraron karin bayani sai a biyomu.
Facebook Forum