WASHINGTON DC, —
Bello Isma'il Garkuwa, dalibi ne da kegudanar da karatunsa a matakin digiri na biyu a jami'ar Abdeen. Inda yake zurfafa karatu a fannin kimiyyar ajiyar bayanai 'Data Science.'
Kasashen da suka cigaba a duniya suna amfani ne da tsarin kimiyyar ajiyar bayanai, wanda ta haka suke tsara abubuwan da zasu so su cimma kaffun shekaru masu zuwa.
A duk lokacin da aka ce kasa tana bibiyar abubuwan da takeyi, kana da tsara jadawali wajen ganin an aiwatar da shi na tsawon wasu shekaru, hakan na taimakawa kasar ta cigaba.
Domin jin karin bayani daga bakin Bello Garkuwa sai a saurari tattaunawar shi da DandalinVOA.
Facebook Forum