Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin mutane 50 suka rasu a hare hare dabam dabam da aka kai a Iraq


Wadansu mutane dauke da gawar wani da aka kashe a harin bom
Wadansu mutane dauke da gawar wani da aka kashe a harin bom
Hukumomin kasar Iraq sun bayyana yau Lahadi cewa, hare hare da aka kai a sassa dabam dabam na kasar sun yi sanadin mutuwar sama da mutane 50 kimanin maitan kuma suka jikkata.

Jami’ai sun ce hari mafi muni ya auku ne a kusa da birnin Amara dake kudancin Iraq, inda wadansu hare haren kunar bakin wake biyu da aka kai suka yi sanadin kashe a kalla mutane 14.

Tun farko a kusa da Balad dake arewacin Bagadaza babban birnin kasar, harin ‘yan bindiga da kuma wani harin bom sun kashe sojoji 11 suka kuma raunata wadansu da dama.

A arewacin kasar kuma, a wani ofishin ‘yan sandan da ake daukar kurata dake kusa da birnin Kirkuk mai arzikin man fetir, ‘yan sandan sun ce wani harin bom ya yi sanadin kashe a kalla kurata bakwai ya kuma jikkata wadansu 17.

An kuma kai hare hare da dama a wurare dabam dabam na kasar Iraq, da suka hada da hare haren bom biyu da aka kai a birnin Nasiriya dake kudanci. Wata fashewar ta auku a kusa da ofishin jakadancin kasar Faransa.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin hare haren.
XS
SM
MD
LG