Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kenya Mutane Kalilan ne Suka Fito Zaben Zagaye Na Biyu


Wapiga kura wasubiri kupiga kura zao katika shule ya Kinyanjui, Nairobi Kenya
Wapiga kura wasubiri kupiga kura zao katika shule ya Kinyanjui, Nairobi Kenya

Hukumar zaben kasar Kenya tace kimanin mutanen miliyan shida da dubu dari biyar ko kuma kashi daya cikin uku na masu rajista ne suka kada kuri’a a jiya Alhamis a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa na shekarar 2017.

An samu rigingimun yan adawa da tashe tashen hankula a runfunar zabe da dama. Akalla mutane biyu ne aka harbe har lahira a wasu arangama tsakanin yan sanda da masu zanga zanga.


Shugaba Uhuru Kenyata yake neman a sake zabensa a karo na biyu a wannan zaben. Kotun kolin kasar ta soke nasarar da ya yi a zaben ranar takwas ga watan Agusta, bayan gano wasu kura kurai da rashin gaskiya wurin aikewa da sakamakon zaben. Kusan kashi tamanin na mutane da suka yi rajista ne suka kada kuru’unsu a zaben na watan Agusta.


Madugun yan adawa Raila Odinga ya janye daga shiga takarar a farko wannan wata, inda yake cewar hukumar zaben kasar bata yi gyare gyaren da yakamata ta yi wurin shirya zaben ba. Odinga ya gargadi magoya bayansa da su kaucewa zaben, wani mataki da ake ganin shine ya tabbatar da nasarar shugaba Kenyatta


Odinga ya fitar da wata sanarwa a jajiberen zaben inda ya dau alkawarin cewar hadakar kungiyoyinsu ta Nationa Super Alliance NASA a takaice ta rikide ta zama kungiyar fafutuka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG