Matsalar fyade na ci gaba da ta'azzara a Najeriya musamman ma a arewacin kasar inda ake samun kananan yara da ake cin zarafinsu.
Wannan ne ya zaburar da kungiyoyi masu fafatukar kare hakkin jama'a musamman kananan yara suka dukufa ga wayarda kan al'umma da bukatar daukar kwararan matakan magance wannan matsalar.
A jihar Kebbi ma batun daya ne domin an samu koke-koke da dama akan cin zarafin kananan yara tamkar yadda shugabar kungiyar fafatukar kare hakkin mata da kananan yara mai suna tallafin mata Zara'u Ahmad ta tabbatar.
Tuni dai da gwamnatin jihar Kebbi ta karba kiraye-kirayen jama'a na daukar matakan magance wannan matsalar inda ta aike da kudurin doka a majalisar dokokin jihar domin amincewa da samar da horo mai tsanani ga masu cin zarafin kananan yara a jihar.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman akan bunkasa al'amuran mata Zara'u Wali ta ce ana sa ran samar da wannan horo zai kawo karshen aikata irin wadannan laifuka a jihar Kebbi.
Da ma akwai dokar kare hakkin kananan yara a Najeriya sai dai bayanai sun nuna cewa jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Arewa da ba su kaddamar da dokar a matakin jiha ba a yankunansu.
Saurara karin bayani daga Muhammad Nasir a sauti:
Facebook Forum