Yanzu haka dai a wani mataki na ba saban ba ko kuma matakin da ba’a taba gani ba, Kasashen yankin kudancin Asiya biyu masu karfin makaman nukiliya kasar India da Pakistan zasu fara wani atisayen soja na hadin gwiwa.
A cikinmakon data gabata ne ministan tsaron India,Nirmala Sitharaman ya tabbatar da cewa India zata bi sahun atisayen yaki da da ‘yan taadda ita da kasar Pakistan.
Sai dai wannan shine karo na farko da za aga kasahen biyu da aka rabu tun a shekarar 1947, sun yarda da juna kuma harma zasu yi wani abu wuri guda karkashin kungiyar kasashen dake yankin kudancin Asiya a Karkashin kulawar Rasha kumaa cikin watan Agustta ne za ayi wannan atisayen
Ita dai wannan kungiyar ta tattalin arziki da tsaro da bunkaa demokaradiyya an samar da it ace a Shanghai na kasar China a shekar 2011, kuma kasashen da sukecikn ta sun hada da China,India,Kazakhastan,Pakistan,Russia,Tajikistan sai kuma Uzbekistan
Facebook Forum