Gwamnatocin kasashen da ke raya tabkin chadi na shirin shigar da wata bukata a gaban majalisar dunkin duniya domin samar da wata dokar da ke baiwa sojojin kasa da kasa shiga yaki da yan Boko Haram.
A yayin wani babban taron shuwagabanin kasashen da akayi ranar talata a jamhuriyar nijer ne shuwagabanin kasashen suka ce kwararru daga kasashensu za su taru domin shedawa kasashen duniya yanda boko haram take, tare kuma da kiran ministocin harkokin wajen kasashen da su gudanar da wani taro a abuja domin shirya takardar da za’a gabatarwa a gaban majalisar dunkin duniya.
Ministan harkokin wajen Nijer Muhammed Bazum ne ya bayana hakan a wata firar da yayi da wakilinmu a Niamey.