Kafar yada labaran kasar Sin ta sanar da cewa an yanke hukuncin shekaru uku na zaman gidan yari akan wani mai binciken kimiyya da ya kirkiri jarirai ta hanyar hada sinadaran halitta.
Kafar yada labaran kasar na Xinhua ne sanar da haka.
Har ila yau kamfanin dillacin labaran Xinhua ya ruwaito cewa, an ci tarar wani mai hada manguguna da masu binciken kimiya.
An kuma ci taran, He Jiankui, Yan miliyan 3 kwatankwacin euro 430,000 kan amfani da magani ba tare da lasisi ba.
Kafar Xinhua ta ruwaito an bayyana masu laifin da cewa ba su da horon karatu akan ililim likitanci, don haka sun taka dokar da ke da alaka da likitoci da masu binciken magani na kasar Sin.
Kotu ta ce an samu masu binciken ne da laifin haifan jarirai 3 ta hanyar hada sinadaran halitta, wanda mata su ka haife.
Xinhua ta ruwaito cewa an rufa batun ga al’umma ne domin samar da sirri.
A shekarar 2018 ne wanda ya jagoranci lamarin ya ce ya yi aikin canja yanayin halittan dan tayin wasu tagwayen mata da aka haifa a cikin wata daya, hakan ya girgiza masana kimiyyar likitanci.
Facebook Forum