Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Netherlands ta janye tallafin da take ba Rwanda


Wani sojan kasar Kwango
Wani sojan kasar Kwango

Kasar Netherlands ta dakatar da tallafin dala miliyan shida da take ba Rwanda bisa zargin cewa, Rwanda na goyon bayan tada kayar baya

Kasar Netherlands ta dakatar da tallafin dala miliyan shida da take ba Rwanda bisa zargin cewa, Rwanda na goyon bayan tada kayar bayan da ‘yan tawaye su ke yi a makwabciya Damokaradiyar jamhuriyar Kwango.

Netherlands ta dauki wannan matakin ne a matsayin maida martani ga rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya zargi gwamnatin shugaba Paul kagame da goyon bayan ‘yan tawaye dake gabashin Kwango.

Kasar Rwanda dai ta musanta zargin ta kuma bayyana matakin da kasar Netherlands ta dauka a matsayin riga mallam masallaci. Amurka ita ma ta janye tallafin da take bayarwa na aikin soja a Rwanda da ke cin dala , yayinda Birtaniya, kasar da tafi kowacce bada tallafi a Rwanda ta jinkirta bada tallafin dala miliyan 25 na watan Yuli, sabili da zargin da aka yi a rahoton da wata tawagar kwararru ta Majalisar Dinkin Duniya ta rubuta.

Shaidar da aka bayar a rahoton da ya nuna hannun gwamnati a tashin hankalin na kasar Kwango ya hada da zargi da wani manomi dan kasar Kwango ya yi cewa, dakarun gwamnatin kasar Rwanda sun yi mashi tambayoyi yana aiki a gonarshi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG