Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Paris-Saint German, dan kasar Brazil Neymar, yana cigaba da fuskantar kalubale bayan da hukumar tattara
harajin kasar Brazil ta kwace wasu gine-ginen mallakar dan wasan da wasu kadarorinsa, saboda samunsa da laifin shafe tsawon wasu lokutta ba tare da biyan haraji a kasar ba.
Hukumar ta bayyana cewar adadin harajin da Neymar ya kaucewa biya sun kai fam miliyan 14, hakanne yasa ta kwace gine-ginen da wasu kadarori akalla da suka kai guda 36.
Jami’an tattara harajin na kasar Brazil, sun bayyana cewar tarin harajin da ake bin Neymar tun a shekarar 2013, lokacin da ya koma Barcelona ta kasar Spain daga kungiyar Santos.
Hukumatar tace duk da kwace wannan kaddarorin ba wai yana nufin dan wasan ba zai yi amfani da su bane, yana da damar da zai amfani dasu, amma matakin ya haramta masa sayar da su ko kuma sanya su cikin wata huldar kasuwanci da zai yi.
Bayan tuhumar almundahanar kin biyan harajin da Neymar ke fuskanta a baya bayan nan, akwai zargin da ake masa na aikata fyade ga wata mata, duk da dai dan wasan da yafi kowa tsada a duniya ya musanta, wannan zargin da ake masa.
Facebook Forum