A ranar Laraba 1 ga watan Yuli Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune ya fidda sanarwar yin afuwa ga wasu masu zanga-zangar adawa da suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika a shekarar 2019, a cewar fadar shugaban kasar.
Tebboune, wanda aka zaba a watan Disamban da ya gabata, ya riga ya roki masu zanga-zangar da su zabi hanyar hawa teburin sulhu kuma yayi alkawarin daukar matakan biyan bukatunsu don tabbatar da zaman lafiya a kasar dake memba a kungiyar kasashen OPEC da ke fidda man fetur da gas zuwa kasashen ketare.
Ya kuma rubuta kudurin yin canje-canje a kundin tsarin mulkin kasar don inganta 'yancin jama’a da kuma bai wa ‘yan Majalisar Dokokin kasar damar taka rawa sosai.
Za a kada kuri'ar jin ra’ayoyin jama’a game da canje-canjen kundin nan gaba a cikin wannan shekarar ta 2020.
Afuwar, wacce ta zo a lokacin da Algeria ta cika shekaru 58 da samun ‘yancin kai, ta hada da wasu masu fafutuka su shida da aka yanke wa hukuncin zama gidan yari saboda laifukan da suka hada da yi wa hadin kan kasar zagon kasa.
Sauran ‘yan kungiyar masu zanga-zangar da yawa da ake kira Hirak, har yanzu suna tsare.
Facebook Forum