Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta bada sanarwar cewa mai tsaron ragar kungiyar David Ospina, na asbiti sakamakon faduwa sumamme da yayi, a lokacin da kungiyar take fafata wasa da takwararta ta Udinese a gasar Seria na bana mako na 28.
Ospina yayi karo ne da dan wasan gaba na Udinese mai suna Ignacio Pussetto, mintuna goma cikin lokacin farko na wasan inda ya samu rauni a kansa.
Sai dai bayan da masu duba lafiya a kungiyar ta Napoli suka dubashi tare da nada masa bandeji, mai tsaron ragar ya iya komawa cigaba da wasan.
Amman bayan mintuna 41, kafin tafiya hutun rabin lokaci, sai aka ga mai tsaron ragar ya fadi sumamme, wanda hakan ya sanya aka gaggauta
garzayawa da shi asibiti, inda har yanzu ake cigaba da bashi kulawa ta musamman.
Mai tsaron ragar David Ospina mai shekaru 30, yana zaman aro ne a kungiyar ta Napoli daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila.
Kafofin watsa labaru daga Italiya sun bayyana cewa anyi aiki wajan duba lafiyar sa, amma Ospina zai kasance a karkashin kulawa har na sa'o'i 24 zuwa 48, nan gaba.
Facebook Forum