Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karan Sigari Karan Tsaye Ga Lafiya Da Tattalin Arziki


Wai shin ana iya cewa rayuwar mashaya taba sigari na iya zama daya da ta sauran mutane? Da yawa mashaya basu sha’awar barin zukar taba, haka kuma mashaya taba kan kokarta don ganin sun bar shan taba a lokuta da dama, amma sai angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Kana da masaniyar ire-iren cuttuttuka da kake sakama jikin ka kuwa? Sau da yawa wasu mashayan kan ji jikin su baya masu dadi har sai sun zuki karan sigari kafin su ji rayuwar tayi masu daidai.

Ko mai hakan yake haifarwa ga rayuwar mashayi dama makusantan su? Shan taba sigari na taimakawa wajen Karin raguwar tattalin arzikin mashaya, don kuwa rayuwar suna shiga cikin wani hali, babu wani mashayin taba da lafiyar sa take kama da wandai baya shaye shaye.

Duk da fadakarwa da kamfanonin sigari ke yi na haddura dake cikin shan taba, amma mutane da yawa basu hankaltaba, hakan yasa hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta ware wannan rana don duba da irin illoli da taba kan yi ga rayuwar mashayan da makusantansu.

Hukumar ta ayyana wani hasashen dake cewar nan da shekarar 2025, za’a samu Karin mashaya taba a duniya da zasu kai kimanin mutane biliyan daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG