Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan Hukumomin Najeriya na Neman cin Gashin Kansu


Batun ba kananan hukumomi cin gashin kansu ya haifar da cece-ku-ce, Yayinda majalisun dokoki suka kammala aikinsu

Ga dukan alamu, kammala aiki da Majalisun Jihohi suka yi akan batun ko a baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu ko akasin haka na cigaba da daukan hankali a Najeriya. Domin kuwa Kungiyoyi da ke fafutukar ganin sun sami dogaro da kai sun ce za su cigaba da gwagwarmaya har sai hakar su ta cimma ruwa.

Comrade Nasiru Kabir, jami’in kungiyar kwadago ta kasa, yace lamarin bai zo masu da mamaki ba don yawancin ‘yan majalisun wakilai da dattawa sun yi iya kokarinsu don ganin an ba kananan hukumomi ‘yancin su amma a matakin jiha kuma sai aka sami akasin haka.

Wakiliyar muryar Amurka, Madina Dauda ta tuntubi Dr. Abubakar Ummar, Malamin makaranta a jami’ar Abuja akan batun, sai yace abu ne mai sarkakiya kuma yana ganin gyaran da ya kamata a yi ya fi a ba kananan hukumomi cin gashin kansu, dole ne a yi tanade-tanaden da in an tura masu kudade a tabbatar da an sarrafa kudaden ta hanyar da ya kamata.

A yanzu dai jihohi bakwai ne suka amince a arewa, guda shidda a kudu. Hakan na nuni da cewa ba a sami kashi biyu bisa ukku na jihohin da suka amince ba, saboda haka ba za a ba kananan hukumomi hurumin dogaro da kansu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG