A ranar Alhamis mai zuwa, kamfanin Pepsico zai fara amfani da na'urar mutun mutumi don kai abinci ga dalibai a wurare fiye da 50 a Jami'ar Pacific dake birnin Stockton a jihar California. Dalibai za su iya ba da odar su na nau'in abincin da suke so da suka hada da Baked Lay's, SunChips ko ruwa, da lemun sha ta amfani da manhaja da suka kirkira.
Wasu kamfanoni suna amfani da motocin masu tuka kansu don raba abinci. A watan da ya wuce, kamfanin Kroger ya sanar da cewa zai fara sayar da kayan sawa a cikin mota mai tuka kanta daga wani kantin sayar da kayayyaki a birnin Scottsdale, dake jihar Arizona.
A cewar kamfanin Robby Technologies, wanda ke kera motar mai sarrafa kanta, wannan mutun-mutumin na inji da za'a fara amfani da su a Jami'ar Pacific, suna da saurin gudu har na kimanin kilo mita 10 a kowane awa. Ma'aikata uku zasu dinga kula da ayyukan na'urorin da suka hada da maye gurbin baturan su idan sun mutu.
PepsiCo ya ce yana gwada aikin ta wannan hanya don wadatar da abokan hurdarsa, da ganin abincin shi ya kai ga mafi yawan abokan cinikisa.
Facebook Forum