WASHINGTON, DC —
Shirin Kallabi na wannan mako ya tattauna akan wata dabi’a da zamani ya gaza canzawa a wadansu kasashe wato auren dole! duk da yake a hukumance ana daukar auren dole a matsayin cin zarafi ko take hakkin dan adam, amma har a wannan karnin akwai kasashe da dama da ake samun iyaye da su ke yi wa ‘ya’yansu musamman mata auren dole.
Wannan dabi’ar na barazana ga rayuwa da makomar ‘yan Mata da Mata a fadin duniya, sau da dama, matan da aka yi masu auren dole su ka yin kokarin gudu daga gidajen auren, wadansu kuma su shiga duniya, yayinda wadansu suke kashe kansu.
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna