Jam'iyyar ta daga kara game da shubancin APC a jihar ta Kaduna da nuna cewa akwai tsare-tsaren da suka yi hannun riga da cigaban al'ummar jihar.
Taron wanda shi ne na farko tun bayan da jam'iyyar ta sha kashi a zaben da ya gabata ya samu halartar manyan 'yan jam'iyyar daga duka kananan hukumomin jihar.
Tsohon kwamishanan ilimi na jihar Alhaji Suleiman Lawal Karushi shi ya karanta jawabin bayan taro. Yace taron ya duba abubuwan dake faruwa a Kaduna tun lokacin da gwamnatin yanzu ta kama aiki. Yace gwamnatin bata amince da hanyar cefanar da hakin 'yan jihar ba. Wai an dauko wasu daga wasu wurare ana basu mukamai maimakon a ba 'yan asalin jihar.
Jam'iyyar ta lura an yi wasu rushe-rushe da suka sa mutane cikin wahala. Wata tsohuwa ma da aka rushe gidanta sai ta mutu nan take. Gwamnatin ta ki biyan mutane albashinsu akan lokaci.
Alhaji Rabiu Bako shugaban wata kungiya ta dattijan jam'iyyar PDP yace jam'iyyarsu bata yiwa kowa laifi ba. An nemi canji amma ba canji mai alheri ba ne. PDP a jihar Kaduna bata rushe gidan kowa ba. Bata kori kowa daga aiki ba kuma bata yiwa mutane ritaya kafin lokacin ritayarsu ta yi ba.
Shi kuwa tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Alhaji Shehu Usman yace watan tona asirin APC bai tsaya ba tukunna. Yace a bari su shiga rami sosai.
Amma mukaddashin jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar APC a jihar Onarebul Salisu Tanko Usono yace duka halin da jama'a suka samu kansu a jihar jam'iyyar PDP ce ta dulmuya mutane cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin jihar. Yanzu gwamnatin APC tana faman gyara barnar da PDP ta yi ne. PDP ta bar ma gwamnatin jihar bashi mai dimbin yawa.
Ga karin bayani.