Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada a Yi Angulu da Kan Zomo


‘Yan Takarar Shugabancin Kasa na APC Janaral Buhari
‘Yan Takarar Shugabancin Kasa na APC Janaral Buhari

Manyan jami'an kemfen din Janaral Buhari suna ganin PDP tana shure-shure ne

Injiniya Sa'ad Abdullahi Majidadin Gombe yace idan har za'a gudanar da zabe cikin adalci ya bugi kirjinsa cewa APC ce zata lashen zabukan.

Yace batun yin angulu da kan zomo bashi da wani ma'ana. A tsaya ayi APC daga sama har kasa domin shi ne zai taimaki Janaral Buhari ya kwato ma arewa 'yancinta, a dawo da dimokradiya.

Injiniya Sa'ad ya cigaba da cewa a duba gidajen da aka kafa tun zamanin Lord Luggard duk sun sayar dasu kuma sun sace kudaden. Sun sayar da duk kamfanonin gwamnati sun kuma wawure kudin.Tun lokacin da Obasanjo ya kama mulki kudin man fetur yayi tashin goran zabi a kasuwar duniya amma babu kudaden yanzu domin an sace. Talakan Najeriya bai damesu ba sai sata.

Ya kira a hada karfi da karfe da Janaral Buhari domin a fidda kitse daga wuta.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG