Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Mahama Ya Karbi Rantsuwar Kama Aikin Shugaban Kasa A Karo Na 2


Haka kuma, an rantsar da mataimakiyar shugaban kasa, Farfesa Jane Opoku-Agyemang, mace ta farko da ta taba rike wannan mukami a Ghana.

A yau Talata, John Dramani Mahama ya karbi rantsuwar kama aikin Shugaban Ghana a karo na 2 a wani biki daya gudana a Accra, babban birnin kasar da ke yammacin Afirka.

John Mahama ya gaji Nana Akufo-Addo, wanda ya bar mulki bayan shafe wa’adi 2.

“Sake zabena wani al’amari ne mai cike da tarihin da ya cancanci maimaitawa,” a cewar sabon shugaban kasar mai shekaru 66 yayin rantsar da shi a gaban dandazon jama’a na Independence Square inda ya kara da cewar “yau mun samu damar sake fasalta kasarmu.”

Haka kuma, an rantsar da mataimakiyar shugaban kasa, Farfesa Jane Opoku-Agyemang, mace ta farko da ta taba rike wannan mukami a Ghana.

Mataimakiyar Shugaban Ghana
Mataimakiyar Shugaban Ghana

Shugabannin kasashen Afirka 20 ne suka halarci bikin da suka hada da Bola Ahmed Tinubu (Najeriya), Bassirou Diomaye Faye (Senegal), Ibrahim Traoré (Burkina Faso), William Ruto (Kenya), Félix Tshisekedi (Jamhuriyar Dimokraddiyar Kongo), Brice Oligui Nguema (Gabon), Julius Maada Bio (Saliyo), da Mamadi Doumbouya (Guinea).

Matsalolin tattalin arziki a kan yadda za’a cece al’ummar Ghana mutum miliyan 34 daga matsalar tsadar rayuwa ne suka mamaye yakin neman zaben na 2024.

Saurari rahoton Hawawu Abdul Karim:

John Mahama Ya Karbi Rantsuwar Kama Aikin Shugaban Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG